Recipes easy to make Wainar gero ta musamman

Recipes easy to make Wainar gero ta musamman

The ingredients for making Recipes easy to make Wainar gero ta musamman

 1. Gero surfaffe gwangwani 6
 2. gwangwani Dafaffen gero Rabin
 3. Yist babban cokali 2
 4. Dakakken karkashi cokali 2
 5. Dakakkiyar kubewa cokali 1
 6. 4 Magi guda
 7. Gishiri Dan kadan
 8. 1 Albasa Babba guda
 9. Man suya
 10. Kabeji rabi
 11. 2 Tumati manya guda
 12. Cucumber
 13. 1 Korean tattasai Babba guda
 14. Garin Kuli kuli Wanda ya sha kayan hadi

Step-step making Recipes easy to make Wainar gero ta musamman

 1. A sami gero a surface a cire dusar sannan a wanke shi a rege a fitar da tsakuwar sai a jika shi na mintuna 30.

  Wainar gero ta musammanmatakin girki1 hoto
 2. Sannan a yi amfani da blender me karfin markade a markada yayi laushi sosai, ko a kai inji a markado.

  Wainar gero ta musammanmatakin girki2 hoto
 3. Idan an markado sai a zuba yist a juya sosai a tabbatar ya samu. Sannan a rufe a dakashi a rana ko GU me dumi ya tashi na tsawon awa 2 ko fi.

  Wainar gero ta musammanmatakin girki3 hoto Wainar gero ta musammanmatakin girki3 hoto
 4. Bayan ya tashi sai a dauko za a ga yayi kwai a ciki alamar ya tashi kenan. Sai a kawo karkashi da kubewa a zuba a ciki

  Wainar gero ta musammanmatakin girki4 hoto Wainar gero ta musammanmatakin girki4 hoto
 5. Sannan a zuba dafaffen gero a ciki a juya sosai, sai a zuba albasa da magi da gishiri a juya Idan ya juyi sai a dandano naji Idan akwai tsami sai a saka bakar hoda karamin cokali 1 a juya.

  Wainar gero ta musammanmatakin girki5 hoto Wainar gero ta musammanmatakin girki5 hoto Wainar gero ta musammanmatakin girki5 hoto
 6. A Dora tanda (kaskon yin waina) a zuba mai Idan yayi zafi sai a dunga zuba kullin a ci. Idan ya soyu sai a juya gefe. A dunga kwashewa a kwano ko roba ta sha iska har a gama.

  Wainar gero ta musammanmatakin girki6 hoto Wainar gero ta musammanmatakin girki6 hoto Wainar gero ta musammanmatakin girki6 hoto
 7. A wanke kabeji, Korean tattasai, tumatir, guriji da albasa a yayyankasu yanda ake so a tsane a kwalanda. Sai a sami kwano a zuba wainar, sannan a barbada mata kuli kuli sannan a yaryada mai.

  Wainar gero ta musammanmatakin girki7 hoto Wainar gero ta musammanmatakin girki7 hoto
 8. Sannan a zuba kabeji, tumatir, Korean tattasai, albasa da guriji. Sannan a sake saka wainar, a barbada kuli a zuba mai sannan kayan kabejin haka za ayi har a zuba yawan da ake so.

  Wainar gero ta musammanmatakin girki8 hoto Wainar gero ta musammanmatakin girki8 hoto
 9. Shikenan sai a rufe. a ci ta da kunu ko da lemo tanada dadi sosai.

  Wainar gero ta musammanmatakin girki9 hoto Wainar gero ta musammanmatakin girki9 hoto