Recipes easy to make Masa da miyar taushe $ miyar naman kaza

Recipes easy to make Masa da miyar taushe $ miyar naman kaza

The ingredients for making Recipes easy to make Masa da miyar taushe $ miyar naman kaza

 1. Hadin masa:
 2. Shinkafa
 3. Yeast
 4. Baking powder
 5. Sugar
 6. Mai
 7. Hadin miyar taushe:
 8. Alayyahu
 9. Kabewa
 10. Ruwan naman kaza
 11. Albasa
 12. Attaruhu
 13. Maggi
 14. tafarnuwa Garin
 15. Manja
 16. Curry
 17. Hadin soyayyan miyar kaza
 18. Attaruhu
 19. Albasa
 20. Tumatur manja
 21. tafarnuwa Garin
 22. Maggi
 23. Gishiri
 24. Manja
 25. tafarnuwa Garin
 26. Garin citta
 27. Nama

Step-step making Recipes easy to make Masa da miyar taushe $ miyar naman kaza

 1. Hadin miyar kaza: zaa cire hancin kayan miya,a bare albasa a yanka kanana a wanke da ruwa a markada su sannan a juye markadan cikin tukunya a dora a wuta abarshi ya dahu sosai har sai ruwan ya kone sannan a sauke a aje agefe.

 2. A gyara naman kaza a wanke a zuba cikin tukunya sannan a zuba yankakken albasa garin tafarnuwa citta a cakuda sai a rufe a barshi ya tafasa sai a sannan a sauke a tsame naman daga cikin ruwan a.zaa dora mai a wuta idan yayi zafi sai a soya wannan naman har a gama. Zaa dora tukunya a wuta a zuba manja idan yayi zafi sai a zuba dafaffan kayan miya ciki a gauraya sannan a zuba maggi curry kadan sai a kawo soyayyan nama a juye ciki a gauraya sannan a rufe a barshi ya dan dahu sai a sauke.

 3. A wanke shinkafa sai ajika ta jiku a wanke sannan a markada. Zaa juye markadan a cikin tukunya ko bokitin roba a zuba yeast suga a gauraya sannan a rufe a barshi wajan dumi ya tashi sannan a zuba baking powder kadan a gauraya sai a dora tanda kan wuta a zuba mai cokali daya ko biyu sannan a zuba kullin da ludayi a soya har sai yayi sannan a juya shima cikin ya soyu.

 4. A bare kabewa a yanka yadda akeso sai a wanke ta a zuba a cikin tukunya a dafa ta dahu sannan a tsame a wanke kayan miya a hada a markada gaba daya.zaa juye markadan cikin tukunya a dora a wuta a zuba manja maggi ruwan naman kaza garin tafarnuwa a barshi ya tafasa sai a yankakken wankakken alayyahu a gauraya sai a sauke tururin zai karasa dafashi.