Recipes easy to make Dambun kaza me dadi

Recipes easy to make Dambun kaza me dadi

The ingredients for making Recipes easy to make Dambun kaza me dadi

 1. 7 Attaruhu manya guda
 2. 5 Kajin gidan Gona guda
 3. 5 Albasa manya guda
 4. Dandano yanda zaiji
 5. Curry cokali 2
 6. Spices cokali 2
 7. Seasoning me hadin harbs cokali 1
 8. Tafarnuwa domin bukata
 9. Dakakkiyar citta me kayan kamshi cokali 1
 10. Man suya
 11. Fennel seed Dan kadan
 12. 6 Lemon tsami manya guda
 13. 1 Danyar citta karama guda
 14. Ganyen parsley sbd ado

Step-step making Recipes easy to make Dambun kaza me dadi

 1. A wanke kazar ayi mata yankan gida 4 sannan a saka lemon tsami a sake wankewa a tabbatar ta fita an fitar da duk dattin da yake jikinta. Sai a tsane a kwalanda. Idan ya tsane sai a juye a tukunya. A zuba yankakkiyar albasa a raba lemon tsami 2 a zuba a ciki.

  Dambun kaza me dadimatakin girki1 hoto
 2. Sannan a wanke attaruhu shima a zuba akai

  Dambun kaza me dadimatakin girki2 hoto
 3. A goga danyar citta a zuba akai.

  Dambun kaza me dadimatakin girki3 hoto
 4. Sannan a saka curry, spices, seasoning, garin citta, hade da Maggie.

  Dambun kaza me dadimatakin girki4 hoto
 5. Sai a daka tafarnuwa Idan ana bukata a zuba akai, a watsa fennel seed sannan a Dan zuba ruwa kadan a rufe sai a Dora akan wuta.

  Dambun kaza me dadimatakin girki5 hoto
 6. A barta ta dahu sosai har ta fara farfashewa, sannan a bari ruwan ya kafe a jikin naman sai a sauke.

  Dambun kaza me dadimatakin girki6 hoto
 7. Sannan a sami karamar tabarya a dunga daddaka naman ya daku ba sosai ba dai. Sannan ba a cire kashin a haka zaki barta. Sai ki samu tray ki juye ki baza ya sha iska. A kula a wajen dahuwar zaki saka wadataccen magie yanda ba sai an kara daga baya ba.

  Dambun kaza me dadimatakin girki7 hoto
 8. Sai a Dora kaskon suya a wuta ayi amfani da me Dan girma, a zuba mai madaidaici a kawo albasa a zuba Idan yayi zafi sai a kwashe albasar a zuba naman a ciki a barbada kori sai a fara juyawa.

  Dambun kaza me dadimatakin girki8 hoto
 9. Ai ta juyawa amma sai anyi hakuri sbd Idan aka barshi suyar ba zatayi kyau ba. Idan ya fara kumfa to alama ya fara soyuwa ne, sai a cigaba da juyawa za abi kamshi yanata tashi.

  Dambun kaza me dadimatakin girki9 hoto
 10. Da zarar naman ya bar jikin kunfar man to shikenan dambun ya soyu sai a kashe.

  Dambun kaza me dadimatakin girki10 hoto
 11. Sannan a juye dambun a kwalandar karfe a dunga dannawa man ya ragu, sai A sami babban faranti me karfi Wanda bazai fashe ba, ko na silver ne sai a shimfida abin tata akai, sannan a juye dambun akai.

  Dambun kaza me dadimatakin girki11 hoto
 12. Daga nan sai a nannade shi kamar za a matse kulli sannan a Dora abu akai ni nayi amfani da murfin tukunya…. Sai a kuma Dora abu me nauyi kamar turmi a danne, za a ga man yanata fitowa.

  Dambun kaza me dadimatakin girki12 hoto Dambun kaza me dadimatakin girki12 hoto
 13. Idan aka matse man sai a mayar da naman cikin turmi a Dan daddaka shi sama sama.

  Dambun kaza me dadimatakin girki13 hoto
 14. Sannan a juye a babbar roba, Idan ya sha iska zaki iya rage kashin ko kuma ki barshi Dan shima yanada dadin ci.

  Dambun kaza me dadimatakin girki14 hoto
 15. Dambun kaza ya kammala.

  Dambun kaza me dadimatakin girki15 hoto Dambun kaza me dadimatakin girki15 hoto
 16. A ci dadi lafiya.

  Dambun kaza me dadimatakin girki16 hoto